Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi jihohin ƙasar 18 kan barazanar ɓarkewar cutar Kwalara saboda barazanar fuskantar ambaliya, sakamakon ci gaba da ruwan sama da ake yi a jihohin.
Alfijir labarai ta ruwaito ministan ruwa da tsaftar muhalli na ƙasar, Joseph Terlumum ne ya bayyana damuwar a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce kawo yanzu mutum 63 ne suka mutu sakamakon ɓullar cutar, yayin da aka samu mutum 1,102 da ake zargi sun kamu da cutar.
Mamakon ruwan sama da ake samu a baya-bayan nan a wasu jihohin ƙasar na ƙara fargaba a zukatan jama’a kan ƙara bazuwar cutar, lamarin da ya sa ministan ya yi kira ga jihohin da su ƙara ƙaimi wajen tsaftace magudanar ruwa, don kauce wa ambaliya.
“Muna kira ga jihohi da ƙananan hukumomi su ƙara ƙaimi wajen tsaftace muhalli domin kauce wa ambaliya da sauran bala’o’in da ke tattare da ambaliya, kamar cutar kwalara”.
Jihohin da ministan ya ce suna fuskantar barazanar ambaliyar sun haɗa da; Akwa Ibom da Anambra da Adamawa da Benue da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da Jigawa da Kogi da Kebbi da Kaduna da Niger da Nasarawa da Ondo da Ogun da Rivers da Taraba da kuma birnin tarayya Abuja.
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj