Hukumar Tace Fina-Finai Dab’i ta jahar Kano zata saka kafar wando daya da masu ywa Baburan Adaidaita Sahu zanen Kwarangwal Da kalaman Rashin Da a.
Alfijir labarai ta ruwaito shugaban Hukumar. Abba El-mustapha ne ya nuna taikaicin sa tare da shan alwashin saka kafar wando daya da duk wani mai sana’ar zane dake yawi matuka baburan Adaidaita Sahu zanen rashin da’a wanda ya hada da hoton kwarangwal ko wata alama ta kungiyoyin tsafi ko rubutun dake nuni da cin zarafi ko kalaman batsa a jikin gine – gine ko ababan hawa musamman babur din Adaidaita Sahu.
El-mustapha na yin wannan jawabin ne a yayin da Kungiyar masu sana’ar zane -zane ta Jahar Kano (Kano State Artist Association) ta kawowa Hukumar sa ziyara karkashin jagorancin Malam Muhammad Kabir da zummar kulla alakar aiki ta yadda zasu hada hannu domin bun kasawa tare da tsaftace sana’ar zane – zane a Jahar Kano.
Mal.Kabir ya bayyana cewa a shirye Kungiyar su take na ta bawa Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano dukkan wata gudun mawa domin ta cimma nasarorin aiyukan data saka a gaba.
A karshe Malam Kabir ya godewa Abba El-mustapha dangane da yadda ya mutunta Kungiyar su tare da zaunawa da su a lokacin da yakamata domin nemo hanyoyin da aiyukan su zasu bunkasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj