Justice Simon Amobeda na babbar kotun tarayya dake kano ya kuma yin wani sabon hukunci a yau juma’a.
A cikin hukuncin da ya gabatar, Alkalin ya haramtawa hukumar zabe ta kasa INEC bawa hukumar zabe ta jihar kano KANSIEC sunayen rijistocin masu zaben dake kan kowanne akwatin zabe a fadin jihar kano.
Alkalin ya kuma ayyana Barr. Dalhatu Shehu Usman a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar kano,tare da umartar hukumar KANSIEC da tayi fatali da sunayen yan takarkarun wani bangare da ke ikirarin shygabancin NNPP ya kawo mata muddin ba Dalhatu Shehu Usman ne.
Alkalin ya kuma sake dakatar da hukumar Yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya daga sanya idanu da kuma bada tsaro a zaben da KANSIEN take shirin yi a gobe asabar.


Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj