Daga Aminu Bala Madobi
Jaridar Alfijir Labarai Ta Rawaito wata kotu a Kano ta bayar da umarnin tura mutane biyu da ake zargi da bayar da rahoton ƙarya dangane da kisan da ya faru a Dorayi Chiranci zuwa gidan gyaran hali, domin ci gaba da shari’ar da ake yi a kansu.
Alkalin kotun ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan la’akari da tuhumar da ake musu, tare da bukatar bai wa hukumomi damar kammala bincike cikin tsari da bin doka.
Kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Fabrairu, 2026, yayin da wadanda ake zargin za su ci gaba da zama a gidan yari har zuwa wannan rana.
Matakin da kotu ta dauka ya nuna irin muhimmancin da doka ke bai wa gaskiya da amana a cikin rahotannin da suka shafi manyan laifuka kamar kisa.
“Bayar da rahoton ƙarya ba wai kawai yana karkatar da bincike ba ne, har ma yana iya janyo tsaiko wajen samun adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Haka kuma, tura waɗanda ake zargi gidan yari har zuwa ranar shari’a ta gaba sako ne mai karfi ga al’umma cewa doka ba za ta yi sassauci da duk wanda ya yi yunkurin rudani ko ɓata aikin hukumomin tsaro ba, musamman a lokutan da ake bukatar gaskiya domin kare rayuka da zaman lafiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t