Kiwo: Inganta kasuwancin dabbobi hanya ce ta samun cigaban tattalin arziki…

IMG 113337 22126 1769078028048

Usman Usman Fulani

An bayyana cewar samar da kyakkyawan yanayi na inganta kasuwannin dabbobi wato Kara a fadin Jihar nan wata hanya ce ta inganta tattalin arzikin Jihar Kano.

Shugaban Kungiyar masu sayar da shanu da dillacinsu da sarrafasu da kuma safararsu ta kasa, resehn Jihar Kano,Alhaji Usman Usman Fulani ne ya bayyana haka lokacin kaddamar da shugabannin  Kungiyar na Karamar Hukumar Dambatta yana mai karin gaske akan irin rawar da wannan Kungiya ta ke takawa wajen inganta zaman Lafiya da tsaro da kuma bunkasa tattalin arzikin Jiha da na Kananan Hukumomi  musamman wajen bayar da Kudaden shiga.

Usman Usman Fulani ya ce kaddamar da shugabancin wannan Kungiya a Karamar Hukumar Dambatta zai taimaka matuka wajen daga darajar masaya dabbobi wato kara tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumomin tsaro da duk masu ruwa da tsaki akan harkar kasuwancin sayar da shanu da dillacinsu da sarrafasu da kuma dakonsu daga jiha zuwa wata Jihar.

Kazalika, ya roki Karamar Hukumar ta Dambatta da ta kawo dauki wajen gyaran karar dabbobin musamman samar da bandakuna da cikakken tsaro da gidajen kwana da na wanka domin fatake ta yadda kasuwar za ta cigaba da rike kambunta a matsayin wacce ta yi fice akan harkokin sayar da dabbobi musamman shanu.

Daga nan ya godewa Shugaban Karamar Hukumar Jamilu Abubakar Dambatta wanda Mataimakinsa Sadiq Fagwalawa ya wakilta wajen kaddamar da shugabannin Kungiyar a wannan yankin.

A jawabinsa,Jami’in cibiyar L-Press Abubakar Muhammad Kabir ya sha alwashin ganin wannan kara ta sayar da shanu ta sami tagomashin kayayyakin more rayuwa domin inganta kasuwancin shanun da safararsu da kuma sarrafasu.

Daga nan ya ja kunnuen shugabannin da su rike gaskiya da Adalci a jagorancinsu.

A nasa jawabin Jami’i mai kula da Kano ta Arewa na Kungiyar, Tijjani Ibrahim Zakari ya ce ko shakka babu wannan Kungiya za ta cigaba da hada kan Yan kasuwa masu mu’amala da wajen saye da sayar da shanu domin samun cigaban yankin tare da kira ga masu ruwa da tsaki na Dambatta da su tallafawa wannan Kungiya

Tijjani Ibrahim Zakari ya godewa Hakimin Dambatta,Dr Mansur Dr Muktar Adnan da Shugaban Karamar Hukumar ta Dambatta Jamilu Abubakar Dambatta bisa goyon bayansu wajen kafa ita wannan Kungiya,yana mai bayyana cewar Kungiyar za ta yi aiki tukuru domin samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci a karar shanun.

Da ya ke Jawabi Shugaban Karamar Hukumar wanda Mataimakinsa Sadiq Fagwalawa ya wakilta ya tunatar da sababbin shugabannin irin kalu balen da yake a kansu na hada kan Yan kasuwar tare da gujewa son rai ko son zuciya wajen gudanar da ayyukansu.

Sadiq Fagwalawa ya jaddada goyon bayan Karamar Hukumar ga wannan Kungiya inda ya ce nan bada jimawa ba Karamar Hukumar za ta kawo dauki domin gyara karar shanun.

Da ya ke sanya Albarka ga sababbin shugabannin,Hakimin Dambatta Sarkin Ban Kano, Dr Mansur Dr Muktar Adnan wanda wakilinsa Baba Ado ya gabatar ya taya sabbin shugabannin murna tare da jan hankulansu akan gujewa duk wani abu da ka iya dakile daraja ko mutunci na Kungiya ko na Karamar Hukumar.

Sannan ya jaddada bukatar yin Adalci a tsakanin Yan kasuwa ba tare da nuna fifiko ba, inda yace  “Kasuwa ta kowa ce da bako da Dan gari, dan haka ya zama wajibi ku yiwa kowa adalici har ma idan da hali a fi kyautatawa bako domin alheri ya kawowa garin”

A jawabinsa, na karbar aiki,sabon Shugaban Kungiyar na Dambatta Muktar Dahiru Ibrahim ya sha alwashin gudanar da shugabanci cikin Adalci tare da bin dokokin Kungiya a kowane lokaci.

Sannan ya nemi hadin kan ‘ya’yan Kungiya don cigaban Kungiyar da Karamar Hukumar baki daya.

Muktar Dahiru Ibrahim ya godewa Shugaban Karamar Hukumar da Sarkin Ban Kano,bisa shawarwarinsu da tallafinsu wajen cigaban Kungiyar,haka kuma ya jinjinawa Hukumomin tsaro da su ke a yankin bisa yadda suke basu hadin kai,inda ya tabbatar musu cewar wannan Kungiya za ta cigaba da ayyukanta na inganta kasuwancin dabbobi da safararsu da sarrafasu a yankin ta yin amfani da sababbin dabarun kasuwanci na Zamani.

A yayin taron an kaddamar da katin shaida na Kungiya da kundin gudanar da mulki da makamantan haka.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *