Daga Aminu Bala Madobi
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), a gidan yari na Kuje da ke Abuja har zuwa lokacin da za a saurara da kuma yanke hukunci kan bukatar belinsu.
Alkalin kotun, mai shari’a Emeka Nwite, ya kuma bayar da umarnin tsare sauran wadanda ake tuhuma tare da shi, da suka haɗa da ɗansa Abubakar Malami da kuma ɗaya daga cikin matansa, Asabe Bashir.
Mai shari’a Nwite ya bayar da umarnin ne bayan sauraron hujjoji daga lauyoyin da ke kare shi karkashin jagorancin Joseph Daudu (SAN) da kuma lauyan masu gabatar da ƙara, Ekele Iheneacho (SAN).
Wannan na zuwa ne bayan bankado wasu kadarori da hukumar EFCC tayi datake zargin na sata ne da tsohon ministan ya handame a zamanin mulkin Marigayi Tsohon Shugaban Kasa MUHAMMAD Buhari.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t