Kotu ta Aike Da Wani Malami Da Ya Yiwa Wata Dalibarsa Fyade Magarkama a Kano

 Kotu ta Daure Wani Malami Da Ya Yiwa Wata Dalibarsa Fyade a Kano

Best Seller Channel 

 

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis, ta bayar da umarnin a tsare wani malami mai suna Sukairaj Kabir mai shekaru 38 a gidan gyaran hali bisa zarginsa da yi wa wata daliba fyade yar shekara 15-  mai tabin hankali. 

Solacebase ta ruwaito, Kabir wanda ke zaune a unguwar Rimin Auzunawa da ke Kano, ya ki amsa tuhumar da ake masa na aikata laifuka biyu na fyade da kuma zaluntar yarinyar. 

Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali, sannan ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Janairun 2022, domin ci gaba da yin sharia ri. 

Best Seller Channel 

Tun da farko dai, mai gabatar da kara, Barasta Asma’u Ado, ta shaida wa kotun cewa wadda ake kara ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 2018 zuwa 2021, a unguwar Tudun Yola, Kano. 

Barasta Asma u ta ce wanda ake kara, kasancewar shi malamin aji ne ga yarinyar, ya rinka shigar da ita wani aji na makarantar Islamiyya, da ke Tudun Yola, Kano. tun tana da shekara 12,” in ji ta.

 A cewar mai gabatar da kara, laifukan sun sabawa tanadin sashe na 283 da 238 na kundin laifuffuka.