Wani Mummunan Hadari Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 6, wasu kuma sun jikkata a Zamfara

 Wani Mummunan Hadari Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 6, wasu kuma sun jikkata a Zamfara 

Best Seller Channel ta rawaito, mutane 6 sun mutu yayin da wasu shida suka jikkata a wani hatsarin mota da ta afku a kauyen Tazame da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara ranar Alhamis. 

Hadarin ya afku ne a lokacin da motar bas Sharon da wadanda abin ya shafa ke ciki ta yi karo da wata mota. 

Kwamandan hukumar FRSC a Zamfara, Iron Danladi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Gusau ranar Juma’a cewa motar bas da wadanda abin ya shafa ke tafiya ta nufi Sokoto daga Abuja.

 Ya ce direban motar bas din yana gudun wuce sa a lokacin da ta bugi motar da ita da ta taso daga wancan gefe 

Danladi ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin kwararru na Yeriman Bakura da ke Gusau domin yi musu magani yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa. makamancin haka. 

Wannan sanarwar ta fito ne daga kamfanin dillancin labaran Najeriya

Slide Up
x