Kotu Ta Dakatar Da Shirin Gudanar Da Zaben Majalisar Matan Nijeriya A Kano

Screenshot 20221202 154709 com.facebook.katana edit 16234138425645

Kafatanin matan da ke birane da karkara duk nasu ne, domin basu ware kowa a cikin tafiyar kungiyarsu ba.

Alfijir Labarai ta rawaito wata babbar kotun jahar mai namba 10, da ke zaman ta a unguwar Bompai, ta dakatar da zaben majalisar matan Nijeriya reshen jahar Kano da ake shirin gudanarwa a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba 2023.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a A’isha Ya’u , ta dakatar da gudanar da zaben ne, bayan wasu yayan kungiyar sun shaida wa kotun cewar, wadanda suke shirin gudanar da zaben ba su ne halastattun shugabanni ba.

Hajiya Fatima Usman Danbatta, na daya daga cikin wadanda suka mika kokensu gaban kotun, in da ta yi kira ga yayan kungiyar da su kwantar da hankulansu domin ana bin komai bisa ka’ida, kuma kotu ta dakatar da masu shirin shirya zaben.

Ta kara da cewa har yanzu ba a rushe su ba, balle wasu su bayyana kansu a matsayin jagororin kungiyar dan gudanar zabe.

Fatima ta ce Kafatanin matan da ke birane da ƙauyuka duk nasu ne, domin basu ware kowa a cikin tafiyar kungiyarsu ba.

Court Oder
Court Oder

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *