Kukan Kurciya Jawabi Ne! Allah Ya Rabamu Da Aikin Dana Sani

FB IMG 1698792276146 edit 9652604447484

KE DUNIYA INA ZA KI DA MU.

Yau Talata 21/10/2023 mun je wata Jana’iza a makabartar Abbatuwa dake kofar mazugal, na ga wani abin mamaki da ya tayar min da hankali.

Ana cikin haka sai aka faso wani tsohon Kabari dake jikin sabon da ake tonawa, kwatsam sai aka hango wata farar Leda ‘Dauke da bakaken Layu guda uku a cikinta da aka rubuta sunan wani a jikinta, kuma da alama an dade da yin wannan mummunan aiki, domin da Layun da ledar duk sun fara rubewa.

Babban abin da ya fi bani mamaki shi ne, wani daga cikin masu aikin Kabarin ya ke fadamin cewa “A kwanakin baya ma haka suka ‘Dakko wata Kwalaba a cikin wani Kabari ‘Dauke da kan Maciji da kuma Layu a cikinta”

Allah Ubangiji ya sa mu gama da Duniya lafiya, ya kuma shiryi masu irin wannan mummunar ‘Dabi’a

📸Sani Bala
📸Sani Bala


Sani Bala Zango
( Abu Safwan )

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *