Kotu Ta Umarci INEC Da Ta Bada Dama Ayi Zaben Gwamnoni Da Katin Zabe Na Wucin-Gadi

Daga Aminu Bala Madobi

Alfijr ta rawaito a ranar Alhamis wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta ba da damar yin amfani da katin zabe na wucin gadi, a zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da za a gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake yanke hukunci a karar da wasu ‘yan Najeriya biyu suka shigar na neman a yi amfani da katin zabe na takadda a babban zabe ba tare da katin zabe na dindindin ba.

“An ba da umarnin tilasta wa wanda ake kara (INEC) da ya ba masu kara damar kada kuri’a ta hanyar amfani da katin zabe na wucin gadi.

Kotun ta ce babu wani kaso na dokar, da Kundin Tsarin Mulki na 1999 da kuma Dokar Zabe da ta bayyana cewa PVC ne kawai za a iya amfani da shi, amma dokar da ke karkashin sashe na 47 ta tanadi katin zabe.

Da yake zantawa da manema labarai, lauyan masu shigar da kara, Mista Victor Opatola, ya ce hukuncin nasara ce ga duk ‘yan Najeriya da suka sha wahala wajen yin rajistar zabe,

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya rawaito cewa, bayan yanke hukuncin, yana kan hukumar ta INEC, an kuma hana kowa daukaka kara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *