Daga Aminu Bala Madobi
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da jihar Kano ta shiga cikin dimuwa a shirye shiryen hukumar na gudanar da zabukan a jihar.
Alfijirta Labarai ta rawaito babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya bayar da umarnin wucin gadi na hana jam’iyyun siyasa 19 tsoma baki a zaben kananan hukumomi da ke tafe.
Umurnin kotun na nufin hana dukkan jam’iyyun kawo wani cikas ga harkokin zaben kananan hukumomin Kano da ake dab da gudanarwa.
Wannan umarni da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta nema, ya shafi jam’iyyu 19 da ake kara, da suka hada da wakilansu, da masu yi musu hidima, da kuma sauran ‘yan uwansu. Cikin Jamiyyun sun hada da Accord Party, Action Alliance, All Progressives Congress, Peoples Democratic Party, da kuma New Nigeria Peoples Party.
A cewar umarnin kotun, an haramtawa wadannan jam’iyyu daukar duk wani mataki da zai kawo cikas a yayin shiri ko lokacin gudanar da zaben.
Kotun karkashin umarnin, ta baiwa hukumar zabe ta kano damar cigaba da gudanar da shirye shiryen ta zabukan kananan hukumomi.
Mai shari’a Ma’aji ya jaddada cewa dokar ta wucin gadi za ta ci gaba da aiki har sai an saurari bukatar da aka gabatar a kan karar nan gaba.
Izuwa yanzu kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 10 ga Oktoba, 2024.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da jihar Kano ta shiga cikin dimuwa a shirye shiryen hukumar na gudanar da zabukan a jihar.
Matakin kotun na da nufin tabbatar da gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da samun tasgaro ko tsangwama ba, a yunkurin baiwa ‘yan kasar damar yin amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a ba tare da tashin-tashina ko tsangwama ba.
Kwararren Lauya mai kwarewar SAN, Barista Lurwanu Umar Esq ne ya jagorancin hukumar zuwa wannan mataki.
Da wannan umarnin, babbar kotun jihar Kano ta sake jaddada aniyar ta na tabbatar da doka da oda da kuma kare martabar tsarin zabe.