Kotu ta wanke DCP Abba Kyari kan tuhumar boye kadarorinsa

FB IMG 1772711981761

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a James Omotosho ta wanke tare da sallamar dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari daga tuhume-tuhume guda 23 na zargin kin bayyana kadarori kamar yadda gidan talabijin na TVC ya rawaito.

Hukumar NDLEA ce ta shigar da karar, inda ta tuhumi Kyari tare da ‘yan’uwansa biyu da zargin rantsuwar ƙarya domin ɓoye asalin wasu kadarori.

Sai dai a hukuncin da kotun ta yanke, ta ce NDLEA ta gaza gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da zargin, musamman kan mallakar filaye da ake cewa suna da alaƙa da Kyari.

Kotun ta kuma bayyana cewa masu gabatar da ƙara ba su kawo takardun da ke nuna cewa kadarorin da ke Fountain Estate, Kasana mallakin Kyari ba ne, haka kuma ba a gabatar da hujjojin da ke danganta shi da wasu kadarori a Asokoro, Abuja da kuma Maiduguri a Jihar Borno ba.

A bayanin kariyarsa, Kyari ya ce kadarorin da ke Borno mallakin mahaifinsa ne wanda ya gada tare da ‘yan’uwansa, kuma masu gabatar da ƙara ba su iya karyata wannan ba.

Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin sallamar su baki ɗaya daga zargin.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *