Kotu ta yi watsi da rokon lauyan mawaki Mai dubun Isa na korar karar jikkata tsohuwar matar sa

IMG 175820 071025 1759856319689

Kotun shari’ar musulunci da ke kumbotso ta yi watsi da rokon lauyan Mai dubun Isa na korar karar jikkata tsohuwar matar sa

An tuhumi Usman Muhammad  gaida mai Dubun isa da zargin laifin gwada karfi, cin zarafin da sanadin mummunan rauni wanda ya sabawa kundin laifufuka na shari’ar musulunci ta jahar Kano

A ranar 14 ga watan 8 2025 wata mai suna Sa’adatu Aliyu  Fagge tsohuwar matar sa ta yi korafi a ofishin yan sanda cewa ranar 3 ga watan 10 shakara ta 2023 mujinta Usman Mai Dubun Isa yayi amfani da karfi Inda ya gaura mata mari Sada taga wuta sanadin haka ta dena gani da ido daya sannan ya dinga tumurmusata har sai da ta samu rauni a Spinal cord dinta.

Bayan karanta masa kunshin tuhumar ya musanta dukka tuhuma 3 mai gabatar da kara lauyan gwamanatin Fatima Tijjani Ahmed ta nemi a bada wata rana domin gabatar da shedu

Lauyan da ke kare shi yayi roko karkashin sashi 168, 172 ACJL da sashi 36 35 da asa wanda yake karewa hannun beli wanda ake tuhuma zai biyayya ga duk umarnin Kotu, muna neman Kotu ta sausauta mane beli wanda muke karewa be aikata laifin Kuma bazai aikata wani laifa a gaba

Mai shari’a Mansir Ibrahim Bello ya sanya shi hannun beli bisa sharadi kawo mahaifi ko dan uwa na jini da zai tsaya masa har a gama shari’a dole ya halarci Kotu duk lokacin da za a shari’a bisa lokaci Kuma duk wanda ya karbe shi sai ya halarci Kotu duk ranar da be zo ba Kotu zata karya belinsa haka zalika Kotu tayi umarnin liketoci su bada rahotonin samun matsalar idanta.

Bayan fitowa daga Kotun munji ta bakin Mai kara Sa’adatu, wadda ta bayyana jin dadin ta da Allah ya fara nuna mata adalci da idonta

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *