Daga Aminu Bala Madobi
Mai shari’a na babbar kotun tarayya da ke Abuja James Omotosho ƙememe ya ƙi amincewa da buƙatar da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, ya gabatar na neman a canza masa gidan yarin da yake a Sokoto zuwa wani kurkuku da ke cikin Abuja ko Jihar Nasarawa.
Kanu, ta hannun lauyansa, ya shigar da ƙara ta gaggawa yana neman umarnin da zai saka gwamnatin tarayya ko hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta hanzarta dauke shi daga Sokoto zuwa Kuje a Abuja ko Keffi a Nasarawa domin samun damar bin diddigin ɗaukaka ƙarar da yake shirin yi.
Sai dai a ranar Litinin, mai shari’a Omotosho ya ƙi amincewa da bukatar, yana mai cewa ba za a iya bayar da irin wannan umarni ba tare da jin ta bakin gwamnatin tarayya ba..
Kotun dai ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga Janairu, 2026.
A ranar 20 ga Nuwamba, kotu ta same shi da laifi kan dukkan tuhumar ta’addanci guda bakwai da Gwamnatin tarayya ta shigar, tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t