Kotu tayi hukunci kan Buhari da Emefele game  da sauya fasalin takardun kuɗi

FB IMG 1745916282074

Wata babbar kotun Najeriya da ke Abuja ta kori karar da aka shigar kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ana neman diyar Naira biliyan 1 kan wahalhalun da tsarin sake fasalin Naira na 2023 ya jefa yan Najeriya a ciki.

Alfijir labarai ta ruwaito mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yi watsi da karar bisa hujjar cewa wanda ya shigar da karar bai maida hankali kan shari’ar ba.

Wani lauyan mazaunin Abuja, Uthman Tochukwu SAN ne ya shigar da karar, wanda ya zargi wadanda ake ƙarar da jefa ƴan Najeriya cikin wahala mai tsanani ta hanyar wannan shiri na sake fasalin Naira.

Karar, mai lamba FHC/ABJ/CS/418/2023, ta haɗa da Buhari da babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma tsohon gwamnan CBN, Emefiele, CBN, da wasu bankunan kasuwanci guda biyu a matsayin wadanda ake kara.

Tochukwu ya yi ikirarin cewa sake fasalin kudin Naira ya jawo masa matsala matuka, inda ya yi zargin cewa an tauye masa hakkinsa na ’yancin tafiya da kuma mutuncinsa.

Sai dai kuma wanda ya shigar da karar ko lauyansa ba su halarci zaman ba ko kuma bayar da wani uzuri na rashin halartarsu.

Lauyan wadanda ake kara na uku da na hudu (Emefiele da CBN), Mista Chikelue Amasiani, ya ja hankalin kotun kan yadda mai karar ya ke nuna halin ko-in-kula a kan ƙarar.

Amasiani ya bayar da hujjar cewa tun shigar da karar a 2023, wanda ya shigar da karar da lauyansa ba su nuna wata himma ko kuma da gaske wajen gabatar da karar ba.

Ya bukaci kotun da ta yi fatali da karar.

A wani dan takaitaccen hukunci mai shari’a Ekwo ya amince da rokon lauyan , inda nan take ya kori karar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *