Kotu Tayi Umarnin Bincikar Abdullahi Abbas Shugaban APC Kano

Alfijr ta rawaito babbar Kotun tarayya da ke Kano ta umarci Kwamishinan ƴan sandan jihar ya binciki Alhaji Abdullahi Abbas kan zarge-zargen da ya yiwa ɗan takarar Gwamnan NNPP na hannu a tayar da tarzoma a unguwarsu ta Chiranchi.

A kwanakin baya ne shugaban jam’iyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya zargi Abba Kabir Yusuf da hannu dumu-dumu wajen rikicin daba da ke afkuwa a Chirancin ta ƙaramar hukumar Gwale.

Sai dai Abban ya garzaya Kotu inda yake neman a matsi bakin Abdullahi Abbas kan zarge-zargen da ya yi masa.

Yanzu haka Kotun ta umarci Kwamishinan ƴan sandan Kano da ya binciki shugaban jam’iyyar APC ɗin.

Barrister Bashir Tudunwuzirci shi ne lauyan Abba Kabir Yusuf, ya yiwa Freedom Radio ƙarin bayani a kai.

Tudunwuzirci yace tun a shekarar 2019 ake ta rubuta korafe-korafen akansa musamman kan maganganu da yake ta yi na tada hankali da amfani da ƴan daba da tada hargitsi a unguwar Chiranchi a Kano.

Ya kara da cewa wanda yake wakiltar a shari’ar ya tabbatar da maganganu da suke da kamshin gaskiya akan Abdullahi Abbas din na yadda ake kawo tarzoma a unguwar, wannan dalili kadai ya isa yan sanda ace sunyi bincike Akai, amma Kwamishinan Ƴan Sandan Kano bai yi komai akai ba.

Duba da bai kamata ace ana wasa da rayukan jama a ba da sunan siyasa yasa muna shigar da batun gaban kotu bisa Umarnin dan takarar

Freedom Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *