Kotun shari’ar musulunci tayi umarnin bincikar Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki

FB IMG 1743111069261

Babbar kotun shari’ar musulunci me zamanta a kasuwar kurmi ta bai wa Mataimakin Babban Sufetan ƴan sandan shiyya ta ɗaya ya binciki Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki, dangane da zargin da ake musu na ɓata wa Gwamnan Kano suna.

Tun da fari dai Hon. Amir Abdullahi Kima SSR a Ma’aikatar Shari’a da Ishak Abdul Mataimakin Gwamnan kan fasahar zamani ne suka yi ƙara a kotun ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Abdu Abdullahi Wayya.

Kotun Kuma ta aike musu da sammaci basu bayyana ba, daga bisani suka turo lauyoyinsu tare da bayanin sukar hurumin kotu.

A zaman kotun na yau Mai Shari’ar ya tabbatar da hurumin kotun akan shariar, ya kuma umarci Ofishin ƴan sanda na Zone One dake nan Kano kan su binciki waɗanda ake zargin, sannan su kawo su kotun domin fuskantar shari’ar

Freedom Radio

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *