Hukumomin Bankin Opay sun fito fili sun barranta kansu daga zargin da ake yi cewa su ke cire wa mutane kuɗi daga asusunsu ba tare da izini ba. A makon da ya gabata, shafukan sada zumunta sun cika da korafe-korafe, inda mutane ke nuna hotuna na kuɗaɗen da aka cire musu, abin da ya jefa al’umma cikin ruɗani.A cikin tattaunawar Jaridar Alfijir labarai da masu ruwa da tsaki na Bankin Opay ta fitar, sun ce ba su da hannu ko kaɗan a wannan al’amari, kuma tsarin ta ba ya cire kuɗi daga asusun Kwastomomi sai dai idan akwai umarni kai tsaye daga mai asusun.
“Inde kasan kaci kudin COVID 19 wanda NIRSAL suka baka bashi to ka shirya ganin alert na fitar kudinsu akoda yaushe tunda bashi aka baka ba kyauta.”
Sun ce binciken cikin gida ya nuna cewa duk cire-cire da ake magana a kansu sun fito ne daga wasu hukumomi na waje wadanda dauke da bayanan su na BVN na masu amfani.
Game da wannan tirka tirka, Hukumar Nirsal Microfinance Bank (NMFB) ta tabbatar da cewa “Mutanen da suka karɓi bashin COVID-19 ne ake cire wa kuɗin.
A cewarsu, “ba kyauta aka basu ba,” domin bashin lamuni ne mai sharudda, kuma tsarin dawo da kuɗin an dora shi kacokan da lambobin sirrin su na BVN.
A cewar su don haka, “Duk wanda ya karbi aro ko kuma aka bashin rancen kudin COVID-19 in har yanada banki kowanne iri ne – OPay ko wani banki – an sanya tsarin atomatik kai tsaye za a cire adadin yawan kudaden da ya karba rance lokacin COVID-19 ba tare da sanarwa ba.
Hukumomin bankin Nirsal sun bayyana cewa an tura sakonni da dama ga masu bashin tun kafin a fara cirar kuɗaɗen, amma wasu ko dai ba su karanta ba, ko kuma sun ɗauka cewa ba za a aiwatar da tsarin dawo da kudin ba. Hakan ne ya sa da yawa suka ɗauka cewa Opay ce ke cire musu kuɗi, alhali kuwa tsarin lamuni ke aiki ne kamar yadda aka tsara tunda farko.
Bayan bayyanar wannan gaskiya, al’umma sun fara fahimtar cewa matsalar ba daga Opay ta fito ba.
Hukumomin biyu sun shawarci jama’a da su rika karanta sharuddan lamuni sosai kafin karɓa, tare da neman karin bayani daga ofisoshin Nirsal idan suna da matsala ko rashin fahimta game da yadda ake biyan bashin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t