Kungiyar Masana Zane-Zane ta Najeriya (SNA) Ta Nuna Takaicin Ta Kan Gobarar da Ta Lakume Herwa Heart of Art Gallery

IMG 20251202 WA0159

Sanannan Wajen koyar da fasaha na Herwa Heart of Art Gallery, wacce ta shahara a matsayin babban cibiyar kirkira kuma ta samu lambar yabo ta Outstanding Gallery Award daga Kungiyar Ɗaliban Zane-Zane ta Najeriya (SNA), ta ƙone kurmus a ranar Juma’a data gabata sakamakon abin da shaidun gani da ido suka bayyana a matsayin fashewar hasken rana kwatsam.

Wannan lamari ya tayar da hankulan makota a fadin yankin, ita kuwa Kungiyar masu fasaha ta bayyana wannan babban rashi ne ba ga ‘yan Kungiyar ba kadai harma ga dalibai masu tasowa, asarar a matsayin babbar rashi ga masu zane-zane, masu sha’awar fasaha da kuma al’ummar da ta dade tana ganin wannan gallery a matsayin cibiyar kirkira da adana al’adunmu na Arewa.

A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, Kungiyar masana Zane-Zane ta Najeriya ta mika jajantarwata ga shugabar gallery Herwa Heart kuma babbar jamia a kungiyar, Hajiya Kaltume Bulama Gana (fsna). Kungiyar ta yabeta bisa hangen nesa, jajircewa wajen inganta fasaha, da muhimmiyar gudummuwar da ta ke bayar wajen ci gaban fasahar a Najeriya.

An yaba mata kwarai da gaske wajen jajircewarta dan zaburar da al’ummomi tsawon shekaru, in ji sanarwar wanda wannan babban abundubawa ne ba nata kaɗai ba ne, rashi ne ga dukkan masu fasahar a Najeriya.”

Kungiyar ta kasa wato Nigerian Society of Artist SNA ta kuma tabbatar da cikakkiyar goyon bayanta ga Hajiya Gana a wannan mawuyacin lokaci, tare da tabbatar mata da shirinta na mara mata baya har tsawon lokacin farfadowa da Herwa Heart of Art Gallery. Haka kuma kungiyar ta yi alƙawarin yin aiki tare da ita da sauran masu ruwa da tsaki domin gina sabo, farfaɗo da ayyuka, da ci gaba da tabbatar da gadon kirkira da kirkire kirkire da Herwa Heart of Art Gallery ke wakilta.

Binta Abba,
Sakatariyar Yaɗa Labarai, Kungiyar Ɗaliban Zane-Zane ta Najeriya (SNA).

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *