Kungiyar Kwadago Sun Aike Wa Shugaba Tinubu Sako Kan Mafi ƙarancin Albashi

FB IMG 1717367892511

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa kungiyoyin kwadago za su jira matakin da shugaba Bola Tinubu zai yanke kan shawarwarin da kwamitin uku kan mafi karancin albashi suka Gabatar.

Alfijir labarai ta ruwaito Ajaero ya yi watsi da duk wani mataki da ake shirin ɗauka har sai shugaban kasa ya bayyana matsayar sa kan bukatar da Labour ta nema na ₦250,000 da kuma kudirin Gwamnati na N62,000.

Kungiyar ta NLC ta dage a kan biyan ₦250,000 a matsayin albashin ma’aikata, yayin da gwamnatin tarayya da na jihohi, tare da kungiyoyi masu zaman kansu, suka bayar da shawarar naira 62,000. Kwamitin uku ya mika dukkan shawarwari ga shugaban kasa a ranar Litinin ta hannun sakataren Gwamnatin tarayya (SGF), George Akume.

A yayin da yake jawabi a birnin Geneva na kasar Switzerland a taron kungiyar kwadago ta kasa da kasa, Ajaero ya ce, “An aika da rahotanni guda biyu ga shugaban kasa, kuma kungiyar NLC za ta jira mataki na gaba kan yadda shugaban ya tafiyar da wannan al’amari. NLC ba za ta dauki wani mataki ba har sai shugaban kasa ya yanke shawara. Da zarar ya yi hakan, Majalisar zartaswa ta kasa za ta tattauna tare da yanke shawarar matakai na gaba.”

Ajaero ya soki Gwamnonin jihohin da ke karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya kan ikirarin cewa ₦62,000 mafi karancin albashi da Gwamnatin tarayya ta gabatar Bazai dore ba.

A ranar 7 ga Yuni, 2024, bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya. Ma’aikata sun rage bukatarsu zuwa ₦250,000, yayin da Gwamnati ta goyi Bayan ₦62,000. Bangarorin biyu sun miƙa rahotonsu ga shugaban kasar, Wanda ake sa ran zai yanke shawara Tare da aikewa da kudirin zartarwa ga majalisar dokokin kasar domin kafa sabuwar dokar mafi karancin albashi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *