Kungiyar kwallon Kafa Ta Kano Pillars Ta Ɗauki Sabbin Ƴan Wasa 12

Kano Pillars

Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars wacce ta lashe gasar Firimiya ta kasa har sau 4 a tarihin ta, ta dauki sabbin ƴan wasa domin tunkarar gasar Firimiya ta kasa ta 2024/2025.

Alfijir Labarai ta rawaito an yi bikin gabatar da sabbin ‘yan wasan ne a filin wasa na Sani Abacha a ranar Laraba 4 ga watan Satumba, inda bikin ya samu halartar shugaban kungiyar, Alhaji Ali Muhammad Na Yara Mai Samba.

Kungiyar kwalllon kafan ta dauki sabbin ‘yan wasa 12 wanda hakan ke nuna ta shirya fafatawa a gasar da za a fara a wannan watan.

Daga cikin wadanda kungiyar ta dauka har da masu tsaren gida da suka hada da: Chukuemeka Oniya daga kungiyar kwallon kafa ta Rangers International da Abuchi Okeke daga Sokoto United da Charles Tembe da Remo Stars.

Haka kuma ta dauki yan tsaren baya da suka hada da Mustapha Jibrin da Ogochukwu Gabrial daga Wikki Tourist da Nelson Abiam daga Doma United sai Alhassan Rashid daga Karela United ta kasar Ghana.

Baya ga sauran sabbin ‘yan wasan, kungiyar ta kuma ci gaba da rike ‘yan wasa 20 da take da su.

A ranar Lahadi, 8 ga watan Satumba ne, kungiyar zata fafata a wasanta na Farko na gasar Firemiya ta bana da takwararta ta Ikorodu City daga Legas.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *