Mafi Ƙarancin Albashi: Majalisar dokokin Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kuɗi na N99b

Screenshot 20240718 172457 Facebook

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kwarya kwaryar kasafin kudi na Naira Biliyan 99 domin baiwa gwamnatin jihar damar aiwatar da mafi karancin albashi da wasu ayyukan.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban majalisar dokokin, Alhaji Jibril Falgore, ya ce kasafin zai baiwa gwamnatin jihar damar biyan mafi karancin albashin da kuma gudanar da ayyukan raya kasa.

Sannan ya godewa ‘yan majalisar saboda amincewa da kasafin ba tare da bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa a ranar 20 ga watan Agusta ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar kwarya kwaryar kasafin na Naira Biliyan 99.

Tun bayan sanya hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi na Naira dubu 70, jihohi da dama suka fara kafa kwamitin aiwatar da kasafin.

Jihar Adamawa ce dai, ta zamo ta farko wajen fara biyan mafi karancin albashin.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *