Sowore Yayi Fallasa: “Badaru Ba Fa Murabus Yayi Bisa Radin Kansa Ba, Sallamar Sa Akayi,

IMG 20251202 WA0021

Ya Buɗe Hanya Ga Janar Christopher Musa!”

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban Jaridar Sahara Reporters, kuma ɗan gwagwarmayar demokuraɗiyya, Omoyele Sowore, yayi wata fallasa wadda ta tayar da kura a dandalin sada zumunta bayan ya bayyana cewa Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar ba murabus yayi tsakani da Allah ba — an umarce shi ne yayi murabus ta dole domin a baiwa tsohon Hafsan Tsaro Janar Christopher Musa, damar rike kujerar ministan.

Sowore ya ce akwai cikakkiyar hujja da ke nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yanke wannan shawara ne sakamakon rashin gamsuwa da halin da tsaron ƙasa ke ciki, tare da niyyar sake fasalin ma’aikatar gaba ɗaya.

Baya ga haka, Sowore ya kuma jawo hankalin jama’a kan sabon matsin lamba daga gwamnatin Amurka, ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Donald Trump, keyi wanda ya nuna damuwa game da yadda ake gudanar da musayar bayanan sirri tsakanin Najeriya da Amurka.

A cewar majiyar da Sowore ya ambata, ana cigaba da auna irin rawar da karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ke takawa musamman kan zarge-zargen alaƙarsa da rukunan ’yan bindiga a Zamfara, lamarin da ke janyo damuwa a matakin tsaro na duniya.
Sowore ya ce “duk abin da ake boye zai fito fili nan ba da jimawa ba.”

Yayin da gwamnati ba ta fitar da cikakken martani ba tukuna, wannan sabon bayani da Sowore ya zartar ya sanya wata aya ga fadar gwamnati — domin irin waɗannan tuhumce-tuhumce kan iya jawo sauye-sauye masu zurfi a tsarukan tsaro na ƙasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *