Kungiyoyin Farar Hula Sun Buƙaci EFCC Ta Bincike Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kwankwaso

Screenshot 20240420 112859 Facebook

Kungiyoyin farar hula arba’in da biyar (CSOs) a karkashin tutar Justice for All (JA) sun Buƙaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da ta binciki tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da gurfanar da shi gaban Kotu.

Alfijir Labarai ta ruwaito a wata wasika da ta aike wa hukumar ta EFCC mai dauke da sa hannun Auwalu Ibrahim da Dokta Dave Ogbole a matsayin shugaba da kuma shugaban kungiyar, a madadin kungiyoyin CSO 45, JA ta bayyana wajabcin Gudanar da wannan bincike domin tabbatar da bin diddigin dukiyar jihar Kano, musamman idan aka yi la’akari da irin wahalhalun da al’ummarta ke fuskanta.

Kungiyar ta jaddada buƙatar hukumar EFCC ta duba wasu abubuwa da suka shafi Gwamnatin Kwankwaso da suka hada da yadda ake tafiyar da kudaden kananan hukumomi, kudaden shiga da ake samu a cikin gida, da kuma yadda ake amfani da kudaden da aka samu daga asusun tarayya. 

Kungiyar ta kuma yi kira da a gudanar da bincike a kan yadda aka sayar da kadarorin Gwamnatin jihar Kano, Tare da zargin cewa an samu haramtacciyar riba daga hannun Kwankwaso, da ‘yan uwansa, da abokansa.

Da take bayyana rashin gamsuwa da yadda gwamnatocin baya suka kasa gudanar da bincike kan zargin cin hanci da rashawa, ƙungiyoyin sun bukaci hukumar EFCC da ta gaggauta daukar mataki, inda ta yi kama da binciken da ta ke kan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.  Kungiyar ta bada wa’adin sa’o’i 48 ga hukumar EFCC ta fara gudanar da bincike, sannan ta bukaci a kulle duk wani asusun ajiyar da ke da alaka da Kwankwaso da iyalansa har sai an mayar da kudaden zuwa baitul malin jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *