Kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya kaddamar da fara raban maganin zazzabin cizon sauro ga al’ummar jihar Kano a yau a asibitin Muhammad Abdullahi Wase wanda akafi sanin sa da suna asibitin Nassarawa.
Alfijir labarai ta ruwaito kwamishinan ya kuma bukaci iyaye su bada haÉ—in kai da goyon baya ga jami’an raba wannan magani a gidaje domin samun damar kawar da zazzabin cizon sauro a jihar Kano.
Kwamishinan yace zakuma a raba gidan sauro a lungu da sako na kananan hukumomin jihar Kano baki daya.
Ya kuma hori iyaye dasu guji sayar da gidan sauron da aka basu domin gujewa fushin hukuma kasancewar yin hakan laifi ne.
Dr. Labaran Yusuf yace jihar Kano na daya daga cikin jihohin da akafi samun mutane masu larurar zazzabin cizon sauro.
Ya godewa hukumomin dake tallafawa harkokin lafiya a jihar Kano dama gwamnatin tarayya.
Yace gwamnatin jihar Kano tana iya kokarinta wajen kyautata harkokin lafiya a jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj