Daga Abubakar Balarabe
Kwamitin Wanda yake karkashin Jagorancin Babban Darakta Janar na Cibiyar Samar da Ayyuka ta Kasa Dr. Baffa Babba Dan’Agundi ta fara gudanar da aikin da Tsohon Gwamnan Kano Kuma Tsohon Shugaban Jam’iyar APC na Kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya fara gudanar da zamansa Domin tantance “Yan Hisba da gwamnatin Kano Mai ci a yanzu ta koresu daga aiki Domin nema masu makoma.
Kwamitin Wanda yake da mutum bakwai ya amince da a Samar da wakilci na mutum 44 daga kowacce Karamar Hukuma dake Jihar Kano.
Kananan kwamitocin daga yankunan Kananan Hukumomin sune Zasu tabbatar da jami’an Hisba kimanin mutum dubu Daya (1,000) da Gwamnatin Kano ta Kora daga aiki.
Kwamitin ya amince da sake fitar da wani karamin kwamiti Mai mutum Uku Wanda zai kula da Samar da mutun daya daga kowacce Karamar Hukuma.
Kwamin dai zai sake Zama a karshen wannan mako tare da karbar rahoton karamin Kwamitin da aka kafa Domin dorawa daga inda aka tsaya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t