Labari Mai Dadi: Fiye da ‘yanbindiga 150 sun nutse bayan kwale-kwale ya kife a Sokoto

FB IMG 1774208174197

Rahotanni sun bayyana cewa akalla ‘yanbindiga sama da 150 sun mutu sakamakon nutsewa bayan wani kwale-kwale da ke dauke da su ya kife a yankin Sabon Gida da ke Jihar Sokoto, kamar yadda Zagazola Makamai ya rawaito.

Majiyoyin yankin sun shaida wa Zagazola Makamai cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar, lokacin da jirgin ruwan da ke dauke da dimbin ‘yanbindiga dauke da makamai ya kife yayin da suke kokarin tsallaka wani tafki a yankin.

A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar na tafiya ne a cikin yawa kafin kwale-kwalen ya kife ba zato ba tsammani, lamarin da ya jefa dukkan fasinjojin cikin ruwa.

“Bayanan farko sun nuna cewa da dama daga cikinsu ba su iya iyo ba, wanda ya haddasa yawan mace-mace,” wata majiya ta bayyana.

Rahotannin farko sun nuna cewa babu wanda ya tsira daga cikin fasinjojin, sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Idan aka tabbatar da faruwar lamarin, ana sa ran hakan zai yi matukar tasiri ga kungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a wasu sassan yankin Arewa maso Yamma.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *