Gwamnati ta sha alwashin sanya ido da gudanar da bincike kan hauhawar farashin kayayyaki, tare da daukar tsauraran matakai kan duk kamfanonin da aka kama suna aikata ayyukan Rashin adalci na kasuwa kamar magudin farashi, Tsadar kayayyaki, Da sauransu.
Alfijir Labarai ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Hukumar Masu Kula da Kayyyaki ta Tarayya (FCCPC) ta fitar.
“Hukumar ta (FCCPC) ta fahimci damuwar da ‘yan Najeriya suka nuna dangane da ci gaba da tashin farashin kayayyaki da na ayyuka.
Duk da karin Darajar Naira a kan dala a baya-bayan nan, Masu saye da sayarwa na kokawa kan tsadar kayayyaki ba tare da an samu raguwar farashin ba. Ba za a yarda da wannan yanayin ba, Kuma FCCPC ta himmatu sosai don kare masu amfani Daga cin zarafi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk