Labari Mai Dadi! Matar Gwamnan Katsina za ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai 50 a ƙasar waje

Screenshot 20240305 122356 com.facebook.katana edit 1066080775357

Uwargidan gwamnan jihar Katsina, Zulaihat Radda, ta ce ta tsara hanyoyin da za ta bi domin bada tallafin karatu a kasashen waje ga dalibai 50 da suka cancanta a jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Uwargidan gwamnan ta bayyana hakan ne a jiya Litinin a Katsina a yayin rufe gasar kacici-kacici, gasar muhawara tsakanin makarantu da kuma gabatar da kyaututtuka.

Wata kungiya mai zaman kanta, Ash-shifa Social Development, Education and Health Awareness Initiative ce ta shirya gasar.

Matar gwamnan ta ce: “Tuni, na samu kuma na raba fam 50 ga daliban da suka cancanta a fadin jihar.”

Ta ce an yi hakan ne a matsayinta na uwargidan gwamnan Katsina, sannan kuma mai kula da shirin Renewed Hope Agenda na jihar, shirin uwargidan shugaban kasa, Sen. Remi Tinubu.

“Ba da jimawa ba, za a gayyato ɗaliban da za su yi jarrabawa a Abuja, kuma wadanda suka yi nasara za su karbi dalar Amurka 7,000 kowanne a matsayin tallafin karatu.

“Bugu da kari, an tanadi fom 500 daidai gwargwado kuma an raba wa ’yan asalin Katsina don ba da tallafin karatu a manyan makarantu a Najeriya,” in ji ta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *