Magoya bayan Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, na ci gaba da nuna bacin ransu kan yadda aka sanya shi memba kawai a Kwamitin Yaɗa Labaran Karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC, maimakon nada shi a matsayin Shugaban Kwamitin.
Rikicin ya fi fitowa fili ne a kafafen sada zumunta, musamman Facebook, inda magoya bayan Waiya ke wallafa sakonni da sharhi suna nuna rashin jin daɗinsu.
An dai naɗa tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Muhammad Garba, a matsayin Shugaban Kwamitin, yayin da Sunusi Bature Dawakin Tofa, Daraktan Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, aka naɗa shi a matsayin Sakataren kwamitin.
Wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya bayan jam’iyyar, inda wasu ke kallon lamarin a matsayin raini ga Waiya
Tuni dai magoya bayan Kwamishinan suka fara kiran shugabannin APC da su sake duba tsarin kwamitin domin kauce wa rikici da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t