Majalisar dattawa ta baiwa kamfanin NNPC wa’adin sati biyu suyi bayani kan wasu kuɗaɗe Tiriliyan 210

FB IMG 1770824758594

Kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar dattawa ya bai wa kamfanin mai na ƙasa,NNPC wa’adin makonni biyu domin ya bayyana a gabansa kan zargin rashin daidaito na kudade har N210 tiriliyan a rahotannin bincike.

Kwamitin ya umarci sabon shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, da ya bayyana tare da tsohon shugaban kamfanin Mele Kyari, da sauran manyan jami’ai da masu binciken kudi na waje kafin ranar 29 ga Afrilu, 2026.

Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ya ce bayanan da NNPC ta bayar kan tambayoyi 19 ba su gamsar ba, musamman kan N103 tiriliyan da aka bayyana a matsayin basussuka da kuma N107 tiriliyan da aka ce an kashe.

Ya jaddada cewa dole ne a fayyace yadda aka kashe kudaden dalla-dalla.

Haka kuma, wasu sanatoci sun bukaci a dauki matakin tilasta wa jami’an kamfanin su bayyana, suna mai cewa dole a dauki lamarin da muhimmanci domin kare martabar majalisa da tsarin dimokuradiyya.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *