Majalisar Dattawa Ta Shawarci Tinubu Ya Sake Daukar Sabbin Sojoji.

FB IMG 1763560336944

Daga Aminu Bala Madobi

Majalisar dattawa a ranar Talata ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da daukar sabbin sojoji 100,000 domin tunkarar masu tayar da kayar baya, da ‘yan fashi don magance garkuwa da mutane dake karuwa a makarantu a fadin kasar nan.

‘Yan majalisar sun kuma bukaci da a gudanar da cikakken bincike a kan shirin na Safe School, inda suka nuna shakku kan yadda aka kashe mazan kudaden da aka ware domin shirin duk da hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin ilimi.

Rahotonni sunce an shiga rudani ne sakamakon harin da aka kai a makarantar Sakandaren ’yan mata ta Gwamnati da ke Maga a jihar Kebbi, inda rahotanni suka ce ‘yan bindigar sun kashe mataimakin shugaban makarantar tare da sace dalibai 25.

Muhawarar ta biyo bayan karin neman da Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa) ya gabatar yayin zaman majalisar, wanda ya haifar da zazzafar muhawara kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya jagoranci zaman majalisar daga bisani kuma ya mayar da majalisar zuwa zaman sirri domin tattauna wasu bayanan sirri.

Oshiomhole, yayin da yake jagorantar mika kudirin daukar sabbin ma’aikata da kuma duba harkokin tsaro, ya yi gargadin cewa girman rashin tsaro na bukatar fadada dabarun yaki na rundunar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *