Daga Aminu Bala Madobi
Bayan tsige shi daga Bulaliyar Majalisa jam’iyyar APC ta umarce shi da ya fice daga jam’iyyar
Alfijir labarai ta ruwaito majalisar dattawa, a yau Laraba, ta sanar da tsige Sanata Mohamed Ali Ndume (Borno ta Kudu) a matsayin Bulaliyar Majalisa.
Yayin da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ayyana zaben cire Ndume da baki, ‘yan majalisar dattijai na APC sun amince da tsige shi a matsayin Bulaliyar.
Nan take ama maye gurbin Ndume da Tahir Mungono (Borno North).
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yake sukar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wata wasika da shugabanni jam’iyyar APC, ta aike wa majalisar dattawa, ta bukaci Ndume ya yi murabus daga jam’iyyar ta APC, ya koma kowace jam’iyyar adawa da ya ke so.
Takardar ta samu sa hannun shugaba jam’iyyar na kasa,Dr Abdullahi Umar Ganduje, da Sakataren ta Barista Ajibola Bashiru.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj