Alfijr ta rawaito Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, INEC, ta ce amfani da adireshin IReV wajen yada sakamakon zaben na rumfunan zabukan kasar nan zai zama cikin lokaci, wanda shi ne tabbatar da gudanar da zabe na gaskiya da gaskiya.
Wannan batun na kunshe ne a wani sako da hukumar ta fitar ta shafin Twitter da aka tabbatar a ranar Talata.
INEC ta ce, gudanar da zabe na gaskiya, zai taimaka wajen tabbatar da cewa an bayyana ra’ayin jama’a da zabin su cikin adalci kamar yadda suka zaba.
Hakan ne ya sa Hukumar ta yanke shawarar yin amfani da na’urar IReV don shigar da sakamakon rumfunan zabe nan take don zaben mai taken #NigeriaDecides2023,”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇