
Alfijr ta rawaito Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya koka kan tsadar mulkin Najeriya kamar yadda ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi watsi da kujerun majalisar dattawa, da ta Majalisar wakilai.
Da yake magana a wani shirin gidan Talabijin na siyasa Channels a ranar Laraba da daddare, Shekarau yace Najeriya bata bukatar majalisun biyu karkashin Tinubu.
A cewar Shekarau: “A bar ni, ba mu da buqatar samar da zauruka biyu.
“Yana kashe kasar. Na yarda, mulkin dimokuradiyya yana nufin shiga tsakani da dama, amma yadda ake tafiya yanzu, kusan ‘yan majalisa 500 ne a fadin kasar nan;
Ba na jin muna bukatar wannan da yawa a halin yanzu.”
Mambobin majalisar dokokin kasar su ne Sanatoci 109 da kuma ‘yan majalisar wakilai 360.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Wannan maganar gaskiya ne