Manhajar Google Ta Hadu Da Ƴan Kwanta Kwanta, Jama’a Da Dama Sun Shiga Rudani A Duniya

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito jama a da dama masu amfani da yanar gizo a duniya sun kasa samun damar shiga binciken Google, yayin da wasu ke bayyana bacin ransu bayan da aka aika musu sakon ban hakuri kan faruwar lamarin

Alfijr Labarai

Dubban masu amfani da intanet sun kasa yin amfani da ayyukan Google bayan da katafaren kamfanin ya samu matsala da ba a bayyana ba.

Babban sabis na sa ido Downdetector, wanda ke bin diddigin katsewar ta hanyar tattara rahotannin sashen, ya ce akwai sama da mutane 40,000 da suka ba da rahoton al’amurra da injin bincike mafi girma a duniya a safiyar ranar Talata (9 ga Agusta) ya tattara

Saƙon matsalar da aka samu an turawa wasu masu amfani da manhajar kuma sun karanta

Alfijr Labarai

“Sabar din ya ci karo da wata babbar matsala wadda tayi kama da ƴan kwanta kwanta, kuma sabar ta kasa kammala buƙatar masu amfani da manhajar”

Har yanzu Google bai fitar da wata sanarwa ba kan faruwar matsalar ba, wadanda aka fahimci sun shafi masu amfani da su a kasashe da dama a duniya.

Baya ga injin bincike, Gmail, taswirorin Google da kuma hotunan Google kuma an ce suna fuskantar matsaloli na lokaci-lokaci.

Alfijr Labarai

Mirror Breaking News

Slide Up
x