Manoma Sun Razana A Yayin Da Farashin Shinkafa Ya Sake Rugurguzowa A Kasuwanni

IMG 20251026 WA0267

Daga Aminu Bala Madobi

Farashin shinkafa ya ragu sosai a kasuwannin Legas sakamakon ƙarin kaya da ake shigowa da su ta iyakoki, abin da ya sauƙaƙa wa masu siye amma ya jefa ’yan kasuwa cikin damuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa farashin buhun shinkafa ta gida da ta waje ya faɗi warwas a kasuwannin Legas sakamakon yawan kayan da ake shiga da su birnin.

Rahoton wanda kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya tattara ya ce, a yanzu farashin shinkafa a birnin Legas ba ya wuce daga Naira 55,000 zuwa 70,000.

Rahoton Hukumar Labarai ta Najeriya (NAN) ya bayyana cewa buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 yanzu yana tsakanin N55,000 zuwa N70,000, gwargwadon iri da kasuwa. A farkon shekara, farashin ya kai N85,000 ga na gida da N95,000 ga na waje.

A kasuwanni kamar Oyingbo, Arena (Oshodi), Festac da Mile 12, an ce farashin ya ragu sosai tun daga watan Agusta bayan yawaitar amfanin gona daga Arewa da kuma buɗe iyakokin ƙasa.

Wata ’yar kasuwa a Arena Market, Mrs Precious Okoro, ta koka da cewa suna sayarwa da asara saboda sun siya shinkafa da tsada a baya. Ta roƙi gwamnati da ta tallafa wa manoma domin tabbatar da daidaiton farashi.

Haka kuma wata ’yar kasuwa a Festac, Mrs Edith Nwaruh, ta bayyana cewa farashin “Pretty Lady” yana N57,000, “Mama Africa” N62,000, “Mama Gold” N67,000, yayin da “Big Bull Premium” yake N73,000.

Wasu masu siye sun nuna farin ciki, suna cewa saukar farashin ya zo a daidai lokacin da sauran kayan abinci suka yi tsada. Wata mai saye, Mrs Andriana Okoromaro, ta ce yanzu za ta iya siyan cikakken buhu domin iyalinta.

Sai dai masana sun gargadi cewa saukar farashin na iya zama na ɗan lokaci, saboda rashin tabbas a kasuwa da yiwuwar farashin ya sake hawa kafin ƙarshen shekara.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *