Manta Sabo: Kotu ta samu Nnamdi Kanu da laifin tuhumar ta’addanci da ake masa

FB IMG 1763647469048

Kotu ta samu Nnamdi Kanu da laifi kan tuhumar ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta yi masa

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu jagoran ƙungiyar IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, da laifi a kan tuhumar farko daga cikin tuhumomin ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a kansa.

A hukuncinta, kotun ta ce ta gamsu cewa Kanu ya yi jerin bayanai ta kafafen watsa labarai da nufin tayar da tarzoma da kisa, a cikin yunƙurin neman ballewar Biafra.

Yayin karanta hukuncin, Mai Shari’a James Omotosho ya ce ya dogara ne kan “shaida da ba a ƙalubalanta ba” da masu gabatar da ƙara suka gabatar, wadda bangaren kariya bai iya karyatawa ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *