Masarautar Kano karkashin jagorancin Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ta dakatar da tsarin bikin hawan sallah karama.

IMG 20250327 WA0097

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da hakan Yana Mai bayyana cewa yin hakan ya biyo bayan wasu dalilai.

Yace bayan samun shawarwari da kiraye kiraye daga shugabanni da iyaye da Malamai da Kuma tattaunawa da yan Majalisar Sarki ya zama wajibi a dakatar da hawan Sallah Karama na wannan shekara.

Sarkin yace Hawan Sallah ba abune na ko a mutu ko ayi rai ba, Wanda idan yin hakan zai kawo tashin hankali ko hargitsi da kawo rashin zaman lafiya to ya zama wajibi a hakura dayin hawan.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace a matsayinsa na Sarkin Kano ya dauki alkawarin kiyaye Imani da mutunci da dukiya da zaman lafiyar al’uma Wanda hakan ce tasa yaga dacewar daukar wannan mataki domin kaucewa dukkan wani abu daka iya kawo tashin hankali ko rashin samun zaman lafiya a tsakanin al’uma.

A don haka ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma da sauran masoya suyi hakuri da wannan hukunci da aka zartar domin samun dorewar zaman lafiya a jihar Kano da Kuma kasa baki daya.

Sarkin na Kano yayi amfani da wannan dama wajan kira ga al’uma suyi amfani da lokutan bukukuwan Sallah wajan ziyartar juna domin sada zumunci, inda ya taya al’umar musulmi murna da farin cikin gudanar da azumin watan Ramadan Yana Mai addu’ar samu dacewar Ubangiji daga cikin bayinsa wadanda Allah yake gafartawa dayin rahama tareda karbar ibadar da aka gudanar.

Sa Hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren yada labaran Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *