Masu Yi Don Allah! Gwamnatin Adamawa ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70

FB IMG 1724503325456

Gwamnatin jihar Adamawa ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70 ga ma’aikatanta.

Alfijir Labarai ta rawaito rahotanni sun tabbatar da cewa ma’aikata sun karbi albashin su na wannan watan a jiya Juma’a, kamar yadda yake a al’ada gwamnatin na biyan albashi a duk ranar 23 ga wata.

Fara biyan mafi karancin albashin, cika alkawari ne da Gwamna Ahmadu Fintiri yayi na fara biyan ma’aikatan daga wannan watan na Agusta.

Wani ma’aikaci mai suna Amos Tumba, ya ce “Karin albashin ya fara aiki kuma an tura min”.

Wata ma’aikaciya mai suna Amma Yohanna ta ce ” Eh, sun biya, kuma an samu kari”.

A ranar 19 ga watan Agusta ne dai, Gwamna Fintiri yayi alkawarin fara biyan mafi karancin albashin a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kwadago.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *