Matar Dan Jaridar Da ‘Yan Sanda Suka Kashe Ta Samu Diyyar Dala 78,000

B6

Wata kotu a Kenya ta umarci bayar da diyyar tsabar kudi har Dala miliyan 78 ga matar dan jaridar nan dan Pakistan da ‘yansandan kasar suka harbe a wani shinge kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Alfijir labarai ta ruwaito Arshad Sharif dai mai gabatar da shirye-shirye ne a gidan talbijin kuma ya yi suna kan sukar sojin Pakistan kan rashawa da cin hanci a kasar.

Shugaban Kenya Ya Kori Ministocin Kasar Baki Daya Daga Aiki
Sauya Fasalin Dimokuradiyyar Afirka: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Yada Kwallon Mangwaro Mu Huta Da Kuda
Danjaridar wanda ya rasu ya bar ‘ya’ya biyar ya sha samun barazanar kisa kuma ya sanar da babban alkalin Pakistan, kafin ya tsere ya bar kasarsa zuwa wata kasar domin neman mafaka.

Kisan Sharif dai da ‘yansandan na Kenya suka yi a garin Kajiado ya tayar da hankalin al’umma sannan kuma jan kafar da jami’ai suka yi kan batun ya janyo suka daga jami’an Majalisar Dinkin Duniya inda suka soki hukumomin Kenya da na Pakistan.

FB IMG 1720878777394
Dan Jarida

Leadership Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *