Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan yawan katsewar wutar lantarki da ake fuskanta a ƙasar nan.
Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya amince cewa matsalar ta jawo wahala ga gidaje, kasuwanci da masana’antu, musamman a lokacin zafi.
Adelabu ya ce ana sa ran samun sauƙi cikin makonni biyu masu zuwa, sakamakon gyaran bututun gas da kuma alkawuran masu samar da iskar gas.
Ya kuma ce gwamnati ta kafa kwamiti domin sa ido kan yadda kamfanonin gas ke cika alƙawuran samar da iskar da ake buƙata domin samar da wutar lantarki.
Ministan ya jaddada cewa gwamnati na aiki tukuru domin inganta samar da wuta tare da cimma burin samar da megawatt 6,000 kafin ƙarshen shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa matsalar na da alaƙa da ƙarancin gas, tsofaffin kayayyakin aiki da kuma wasu matsalolin tsarin wutar lantarki a ƙasar.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t