Matawalle ya gargadi Amaechi kan kalaman tunzuri da yake furtawa

IMG 20250201 094601

Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Dr. Bello Muhammed Matawalle, ya yi Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin maganganu marasa hankali da kuma tunzura tashin hankali da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi kan shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wata tattaunawa da aka gudanar a Abuja, an jiyo Amaechi yana cewa dole ne ‘yan siyasa masu “sata, su kashe mutane, su sa a raunata su” domin su ci gaba da rike mulki.

Matawalle ya bayyana wannan kalami a matsayin abin kunya ga ‘yan Najeriya da kuma yunkuri na haddasa fitina da tada hankalin matasa.

Da yake mayar da martani, Dr. Matawalle ya ce: “Abin takaici ne da hadari ga wani tsohon mai rike da mukamin gwamnati ya furta irin wannan magana mai hadari. A lokacin da gwamnati ke kokarin hade kan yan kasa da tabbatar da tsaro, babu wani shugaba mai hankali da zai rura wutar tashin hankali da rikici na siyasa.”

Ya kara da gargadin cewa babu wanda zai samu nasara ta hanyar batawa matasa tunani da jefa su cikin tunanin tashin hankali da rudani. “Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta, wanda dokoki ke tafiyar da ita, ba daji ba ne da za a samu mulki ta hanyar karfi da tashin hankali.”

Matawalle ya ja hankalin Amaechi da cewa dole ne ‘yan Najeriya su sani cewa mulki ana samun sa ne ta hanyar dimokuradiyya, ba ta hanyar tsoratarwa da tashin hankali ba.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar, an jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci kowace irin magana da za ta iya tunzura tashin hankali ko kawo rarrabuwar kawuna a kasa ba.

Matawalle ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Shugaba Tinubu ya kuduri aniyar ci gaba da kare hadin kan kasa da tabbatar da ci gaba a mulkin dimokuradiyya.

Ya kuma jaddada cewa nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin kankanin lokaci sun isa su tabbatar da cewa zai samu nasara a zaben 2027.

A karshe, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bada goyon baya ga Shugaba Tinubu tare da yin watsi da kalaman Amaechi da sauran abokan aikinsa, da ya bayyana a matsayin “wadanda suka rasa tasiri a siyasa kuma ba su san abin da ke faruwa ba dangane da ci gaban kasa.”

ATP Hausa

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *