Gwamnatin Kano za ta kashe biliyoyin Naira don gudanar da auren zawarawa da ciyarwar Azumi

FB IMG 1736432886576

Daga A’isha Salisu Ishaq

Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira biliyan 2.5 domin gudanar da auren zawarawa daga kananan hukumomi 44 na jihar a shekarar 2025.

Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kudi na Jihar, Musa Shanono, ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ‘yan jarida bayani kan yadda kasafin kudin shekarar 2025 da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da shi ya kasu.

Ya kara da cewa daga cikin adadin kudin, an ware Naira biliyan 1 don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan.

Ya kuma ce Naira miliyan 955 an ware ta ne don gudanar da binciken kididdigar ma’aikata, binciken halin da gidaje ke ciki da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Bugu da kari, ya bayyana cewa an ware Naira miliyan 267.6 don samar da kayayyakin more rayuwa da kuma tallafa wa shirye-shiryen Da’awah na addinin Musulunci.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *