Gwamnan jihar Neja, Manomi Mohammed Umaru Bago, ya rusa majalisar ministocinsa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jiha a zauren majalisar da ke Minna.
Ya kuma yaba musu bisa irin ayyukan da suka yi a halin yanzu na ci gaban jihar tare da yi musu fatan alheri.
Gwamnan manoman Bago, yace rushewar bata shafi Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ba, da Shugaban Ma’aikata da Mataimakin Shugaban Ma’aikata, da sauran manyan Mataimaka a ofishinsa.
Masu sharhi sun bayyana wannan sauyi a matsayin wani sabon salo da zai dauki Jihar Neja zuwa sabon matsayi na ci gaba. A yanzu, idon jama’a ya karkata kan yadda wannan sabon tsari zai sauya rayuwar al’umma gaba daya.
Bologi Ibrahim
Babban Sakataren Yada Labarai
ga Gwamnan Jihar Neja
1/9/2025.