Alfijr
Alfijr ta rawaito mazauna Kano sun koka a kan yadda ake kokarin kwace makarantar sakandare din Kofar Nasarawa, wacce aka fi sani da GSS K/Nasarawa
Wasu ganau sun bayyana yadda aka rushe wasu azuzuwa da katangar bayan makarantar don mai da wurin harabar kasuwanci tare da shimfida ginin shagunan.
Hakan yasa mazauna yankin shiga cikin damuwa, duba da yadda makarantar ta kasance daya daga cikin dadaddun makarantu a jihar.
Alfijr
Mazauna da kungiyoyi masu zaman kansu a cikin birnin suna cigaba da kokawa bisa yadda ake gina shaguna a filayen da suke mallakin asibitoci, masallatai, filayen kwallo da makabarta da sauran su.
An tattaro rahotanni a kan yadda aka saida wasu azuzuwa da katangar bayan makarantar gwamnati ta Kofar Nasarawa, wadanda suke kusa da gidan wasa na Sani Abacha ga mutanen don gina shagunan.
Bayan katangar makarantar ya ratsa ta sanan nan titin IBB kusa da kasuwar Kwari, wanda ake ganin shine dalilin siyar da wurin.
Alfijr
Wata majiya ta bayyana Daily Trust ta ziyarci makarantar ranar Juma a, an gano yadda aka shimfida ginin shagunan, wanda motar rusa gini ta rusa wasu bangaren tsoffin azuzuwan makarantar.
Wani ‘dan kasuwa kusa da makarantar ya shaida yadda aka rushe wasu azuzuwa baya ga bangon bayan makarantar. “Mu dai kawai mun ga motar rushe gini tana rushe ginin, inda wasu ke gyarawa gami da shimfidar gini. Maganar gaskiya, ba mu yi tunanin za a kai wannan matakin ba.
Daily Trust ta tattaro yadda makarantar ta kasance daya daga cikin dadaddun makarantu a birnin, yayin da mazauna yankin suka ji tsoro yadda tarihinta ke kokarin rushewa bisa yadda aka mallake wani bangarenta.
Alfijr
Wannan tsohuwar makaranta ce. Dukkanmu mun taso mun ga makarantar a nan ne,
amma yau, suna son gurgunta cigabanta,” a cewar wani mazaunin yankin, Jamilu Saad.
Yayin da ake ta yada cewa gwamanati ta kwace filin don gina shagunan, tare da ikirarin kuskure ne yin ginin, Daily Trust bata samu wani ma’aikacin gwamnati da zai tabbatar da hakan ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.
Kamar yadda Legit ta wallafa