Ministan Birnin Tarayya Ya Dakatar Da Sakataren Ilimi Dallami Hayyo

FB IMG 1764108482254

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu kafafen yada labarai, inda ta ce an umarci dukkan makarantun gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja su rufe nan da ranar 28 ga Nuwamba, 2025.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Lere Olayinka, babban mataimaki na musamman ga Ministan Abuja kan harkokin sadarwa  da kafafen sada zumunta, ya bayyana rahoton a matsayin “karya, yaudara, kuma sam ba gaskiya bane.

Wike ya kuma bayar da umarnin dakatar da Sakataren Ilimi Dokta Danlami Hayyo, kan cece-kucen da takardar ba da izini ta haifar, yayin da aka dora wa mukaddashiyyar shugabar ma’aikata, Mrs Nancy Sabanti Nathan takaddar jan kunne ta ladabtar da daraktan kula da harkokin makarantu, Mrs Aishatu Sani Alhassan, bisa karya ka’idojin aikin gwamnati.

“Ba a yanke irin wannan hukunci gaba-gadi. Ya zama wajibi iyaye, dalibai, da hukumomin makaranta su yi watsi da jita-jita. Kalandar karatun da aka amince da ita ba ta canza ba,” in ji Olayinka.

Gwamnatin ta kuma baiwa mazauna yankin, musamman dalibai tabbacin samun isasshen tsaro a fadin makarantu, tare da bayyana cewa Ministan ya bayar da umarnin a dawo da shirin Operation Sweep da sauran tsare-tsare na tsaro domin karfafa tsaro a babban birnin.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, sakataren hukumar ilimi da aka dakatar, Hayyo, ya nisanta kansa daga takardar da aka ce ya jawo cece-kuce, inda ya ce an fitar da ita ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.

“Hakika, yadda kuka ga ni, nima haka na ganta, domin daraktan da ya sanya hannu ba shi da hurumin yin hakan,” inji shi.

Ya kara da cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja ne kadai ke da hurumin amincewa da rufe makarantu a kowane hali, ya kara da cewa ba a bayar da irin wannan umarnin ba.

Ya bukaci iyaye da su yi watsi da wannan bayanai kuma su ci gaba da ayyukan koyo da koyarwa na yau da kullun, ya kuma yi watsi da jita-jita na rashin tsaro a yankin, yana mai jaddada cewa babu “wata magana gameda rufe makarantu” da aka bayar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *