Wata Sabuwa: Albarusai Sun Zubo Daga Mota Gaban ABU Zaria An Zargin Na ’Yan Bindiga ne

FB IMG 1764165657897

Lamarin ya bayyana a gaban ƙofar babban shigar ABU Zaria a safiyar Talata, lokacin da alburusai suka zube daga wata motar fasinja da ke wucewa kan titin Zaria–Katsina.

Ganau sun ce alburusan sun fito ne daga wata ƙaramar mota mai ɗaukar fasinja da ta nufo hanyar Katsina yayin da ta wuce da sauri a gaban ƙofar jami’ar.

Wani shaidan gani-da-ido mai suna Musa ya ce:

“Kawai muka ga alburusan suna faɗowa daga jikin motar. Kafin mu fahimci me ke faruwa, motar ta gudu”

Wasu matasa da ke wajen sun tattara alburusan, suka kuma sanar da jami’an tsaro da ke kusa da yankin.

Wata ɗaliba ta jami’ar, wadda ba ta so a ambaci sunanta ba, ta bayyana lamarin da “abun tsoro” musamman ganin yadda wasu ke zargin makaman na iya kasancewa cikin kayan da ake safarar zuwa hannun ’yan bindiga da ke addabar Kaduna da Katsina.

Jami’an tsaro daga baya sun iso wajen, suka kwashe duk alburusan da aka gani.

Mikiya

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *