Ministan Isra’ila ya bukaci Yahudawan Birnin New York Su Gaggauta Yin Hijira Zuwa Isra’ila.

IMG 20251105 WA0020

Daga  Aminu Bala Madobi

Zohran Mamdani, Musulmi, Dan Jam’iyyar Democrats, Kuma Dan Majalisar Dokokin Jihar New York, Yayi Shura Wajan Caccakar Manufofin Israela Da adawa Da Abinda takeyiwa Palastine-

Tun bayan nasarar da Dan takarar jam’iyyar Democrat Socialist, Zohran Mamdani yayi, a zaben magajin garin New York.

Ministan kulada da Yahudawa Mazauna wasu Ƙasashe na Isra’ila, Amichai Chikli ya bayyana nasarar Mamdani a matsayin “muhimmin juyin juya hali da koma baya ga birnin New York” wanda, a cewarsa, “ya girgiza tushen wurin da ya bai wa dubban ‘yan gudun hijirar Yahudawa dama da ‘yanci.”

Chikli wanda ya taba bayyana goyon bayansa ga mamayar kudancin Lebanon da kuma gidajen Yahudawa a Gaza — ya kira Mamdani “mai goyon bayan Hamas.”

Ya yi zargin cewa ra’ayoyin Mamdani, wanda ke da shekaru 34 kuma musulmi ne, “ba su da nisa da na masu tsatsauran ra’ayi na jihadi da suka kashe mutane 3,000 shekaru 25 da suka wuce,” yana nufin hare-haren 11 ga Satumba (9/11).

A karshe, ya yi kira ga Yahudawan New York da su “gaggauta komawa Isra’ila.”

Mamdani, wanda dan majalisa ne daga yankin Queens, New York, ya lashe zaben magajin gari a ranar Talata, inda ya zama musulmi na farko da zai shugabanci birnin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *